Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wani taro mai take Qods birnin al'adun larabawa na shekara ta 2009 a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, wanda yake samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen larabawa da na musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; An fara gudanar da wani taro mai take Qods birnin al'adun larabawa na shekara ta 2009 a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, wanda yake samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen larabawa da na musulmi. Rahoton ya ci gaba da cewa har yanzu mahalarta taron na ci gaba da isowa daga kasashe daban-daban, daga cikinsu kuwa har da manyan malamai da kuma jagororin mabiya addinin kirista daga palastinu labanan Syria Jordan da kuma Masar mai masafkin baki. Baki yazu daya kan wajabcin bayar da kariya ga masallacin Qods da ma dukkanin wurare masu lafarma da ke birnin da ke fuskantar barazana daga yahudawan sahyuniya.
417179