Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na attajdid.com cewa; Kimanin manyan malaman addinin Musulunci 52 ne suka fitar da fatawa da ke haramta duk wani mataki sa ido ana kallon yahudawan sahyuniya suna ci gaba da wulakanta masallacin Qods da kuma sauran wurare masu tsarki da ke birnin. A nasa bangaren jagoran harkar Musulunci a yankunan palastinawa da ke gabacin Qods Sheikh Ra'id Salah ya bayyana cewa; wannan fatawa da ta samu sa hannun malamai daga kasashen duniya daban-daban ta bayan haramta sa ido ana kallon yahudawan sahyuniya suna keta alfarmar wurare masu tsarki, a bangare guda kuma ta kirayi musulmi da su motsa domin bayar da kariya ga masallacin mai alfarma. Daga cikin malaman da suka rattaba hannu kan wanna fatawa kuwa har da sheikh Yusuf Kardawi.
417153