Bangaren kasa da kasa: A wani zaman taro da kungiyar hadin kan kungiyoyin larabawa ta gudanar a birnin Bodapost na kasar Filland, ta nuna wani fim da aka dauka a lokacin da Isra'ila ke kai hare-haren kan al'ummar gaza a farkon shekarar nan, wanda ke nuna yadda yahudawa suka yi kisan gilla a kan kanan yara da mata da tsoffi da fararen hula.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana kasar Syria cewa; A wani zaman taro da kungiyar hadin kan kungiyoyin larabawa ta gudanar a birnin Bodapost na kasar Filland, ta nuna wani fim da aka dauka a lokacin da Isra'ila ke kai hare-haren kan al'ummar gaza a farkon shekarar nan, wanda ke nuna yadda yahudawa suka yi kisan gilla a kan kanan yara da mata da tsoffi da fararen hula. Bayanin ya ci gaba da cewa, wanda ya hada wannan fim ya yi tattaki ne zuwa zirin Gaza, inda ya zanta da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Gaza a lokacin da Isra'ila ta yi kisan kare dangi a kansu, inda suke bayar da labari kan mummunan halin da haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya ta jefa su.
417776