Bangaren kasa da kasa; Masu fasaha da ke hada hada kayan al'adu a kasar Italia, sun nuna irin matsanancin zaluncin da palastinawa ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya, a baje kolin kayan al'adu da ake gudanarwa a birnin Rom fadar mulkin kasar Italia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gidan talabijin din almanar da ke watsa shirye-shiryensa daga kasar Labanan cewa; Masu fasaha da ke hada hada kayan al'adu a kasar Italia, sun nuna irin matsanancin zaluncin da palastinawa ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya, a baje kolin kayan al'adu da ake gudanarwa a birnin Rom fadar mulkin kasar Italia. Bayanin ya ci gaba da cewa, daga muhimman abubuwan da aka baje kolinsu a wurin akwai zane-zanen hotuna da ke nuna irin zalunci da danniya da al'u,,ar palastinu ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya, tare da hada wasu gajerun fina-finai dangane da yanayin da al'ummar palastinu suka samu kansu a ciki, sakamakon ci gaba da mamaye yankunansu da yahudawan ke yi.
418903