IQNA

An Fara Gudanar Da Taro Kan Ilmomin Kur'ani A Kasar Bahrain

18:03 - June 13, 2009
Lambar Labari: 1790423
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da zaman taro a karo na uku dangane da ilmomin da ke cikin kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, domin sanin yadda za a warware da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwasat ta kasar Bahrain cewa; An fara gudanar da zaman taro a karo na uku dangane da ilmomin da ke cikin kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, domin sanin yadda za a warware da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a fadin duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar manyan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, daga cikin malaman kuwa har da Ayatollah Muhammad taki Mudarrasi, daga cikin masana da malamai 600 da suke halartar zaman taron. Za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da wannan zaman taro, da nufin samar da hanyoyin da suka d ace daga wajen warware matsaloli da dama da duniya ke fuskanta a mahamnagar kur'ani.

419396
captcha