Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin musulmi a kasar Birtaniya cewa; An gudanar da taron maulidin sayyida Fatima Zahra (AS) a sassa daban-daban na kasar Birtaniya, wanda ya samu halartar musulmi daga ko'ina cikin fadin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro na daya daga cikin taruka mafi girma da al'ummar musulmi da ke kasar Birtaniya suka gudanar, domin kuwa taron ya samu halartar musulmi daga ko'ina cikin fadin kasar. Bayanin ya kara da cewa an gudanar da bayanai a lokacin gabatar da taron, da ke nuni da cewa sayyida Zahra abin koyi ce ga dukkanin musulmi da ma 'yan adam baki daya.
420542