IQNA

An Tattauna Kan Rawar Da Musulunci Zai Iya Takawa A Harkokin Tattalin Arziki

15:47 - June 22, 2009
Lambar Labari: 1793240
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zaman taro wanda ya yi bahasi kan irin rawar da tattalin arzikin musulunci zai takawa wajen shawo kan matsalolin harkokin tattalin arziki da kasashen duniya ke fama da ita, wanda aka gudanar a birnin Riyad na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya was cewa; An gudanar da wani zaman taro wanda ya yi bahasi kan irin rawar da tattalin arzikin musulunci zai takawa wajen shawo kan matsalolin harkokin tattalin arziki da kasashen duniya ke fama da ita, wanda aka gudanar a birnin Riyad na kasar Saudiyya. Taron ya samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki daga kasar saudiyya da kuma malaman jami'a wadanda suka gabatar da makalolinsu da mahangarsu dangane da yadda za a kawo karshen matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, da kuma yadda za a iya yin amfani da mahangar muslunci kan harkokin tattalin arziki da kuma yadda za a shawo duk wata matsala ta wannan fuska.


422808
captcha