IQNA

Wani Musulmi Ya Samu Kyautar Girmamawa Daga Majami'ar Amurka

15:47 - June 22, 2009
Lambar Labari: 1793241
Bangaren kasa da kasa; Wani musulmin kasar Amurka kuma mamba a kwamitin kula da harkokin addinai na jahar Ohayo Abubakar Arman, ya samu kyauta ta musamman da majami'ar birnin Colombos ke bayarwa, bisa kokarinsa na ganin an samu sulhu da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin dukkanin mabiya addinai.
Kamfanin dillancin labran ikna ya nakalto daga jaridar iman ta kasar saudiyya cewa; Wani musulmin kasar Amurka kuma mamba a kwamitin kula da harkokin addinai na jahar Ohayo Abubakar Arman, ya samu kyauta ta musamman da majami'ar birnin Colombos ke bayarwa, bisa kokarinsa na ganin an samu sulhu da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin dukkanin mabiya addinai. Rahoton ya ci gaba da cewa Abubakar Arman ya samu kyautar girmama daga majami'ar ne bayan da malaman majami'ar suka hadu kan cewa shi ne ya fi dacewa da hakan, sakamakon rawar da ya taka wajen shiryar da mutane da dama da suke bin addinai daban-daban, ta yadda za su fahimci juna da sauran mabiya addinai domin a samu zaman lafiya a duniya tare da girmama juna.


422969
captcha