IQNA

Sulhu A Mahangar Addinai A Ranar Farko Ta Taron Otrish

17:25 - June 22, 2009
Lambar Labari: 1793641
Bangaren ilimi da bincike; a ranar farko ta taron kasa da kasa a kasar Otrish kan sulhu da tabbatar da adalci ta hanyar tattauanawa na bai daya an yi dubi ne kan sulhu a addinance.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ce ta watsa rahoton cewa; a ranar farko ta gudanara da taron kasa da kasa day a hada masana da marubuta da malummai da kuma nazari kan addinai an maida hankali ne kan maganar tabbatar da sulhu da wanzuwarsa a mahangar addinai inda mahalarta taron suka yi ta bayani daya bayan daya kan rawar da addini ke takawa wajen shinfida sulhu da zaman lafiya a doran kasa.

423046

captcha