IQNA

An Gudanar Da Wani Taro Kan Ilmomin Kur'ani A UAE

13:46 - June 25, 2009
Lambar Labari: 1794809
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani taro kan ma'anar tunani a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki a birnin Sharjah na kasar Hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran albayan cewa; An gudanar da wani taro kan ma'anar tunani a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki a birnin Sharjah na kasar Hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar malamai dam asana daga sassa daban-daban na kasashen larabawa, wanda suka yi bahasi dangane da ma'anar tadabbur, wato tunani kan ma'nonin ayoyin kur'ani mai tsarki, kamar yadda ya zo a cikin wata ayar kur'ni da ke cikin suratul Muhammad aya ta 24, dangane da wajabcin yin tunani kan ma'anar ayoyin kur'ani mai tsarki, maimakon karanta shi ba tare da yin tunanin ma'anar ayoyinsa ba.

424882


captcha