IQNA

Za A Gudanar Da Taron Maulidin Imam Bakir (AS) A Tronto

13:48 - June 25, 2009
Lambar Labari: 1794810
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da taron maulidin Imam Bakir (AS) a biranan Tronto da kuma Hustan na kasar Canada, wanda cibiyar yada ilmomin ahlul bait ta kasar Canada ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na jaffari cewa; Za a fara gudanar da taron maulidin Imam Bakir (AS) a biranan Tronto da kuma Hustan na kasar Canada, wanda cibiyar yada ilmomin ahlul bait ta kasar Canada ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar mabiya mazhabar shi'a da ke zaune a sassa daban-daban na kasar Canada, da suka hada da masu gabatar da jawabai, da kuma masu gabatar da wakokin yabon manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka. Haka nan kuma a wajen gudanar da taron za a karanta addu'ar nan ta tawassuli da manzon Allah da limaman ahlul bait da kuma sayyid Zahra (AS)

424860







captcha