Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar alwatan ta kasar Saudiyya cewa; An fara gudanar da wani zaman taro na kasa domin yin nazari dangane birnin Qods da kuma msallaci mai alfarma da ke birnin a garin Rammalah da ke gabar yamma da kogin Jordan. Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen gudanar da taro nana tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar bornin Qods da kuma matakan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na mayar da birnin mallakin yahudawa, tare da fitar da duk wani batun larabawa daga abin da ya shafi masallacin Qods da ma birnin baki daya, inda daga cikin matakan da yahudawan suke dauka akwai kokarin rushe wani bangare na masallacin, da kuma rushe gidajen palastinawa da ke gabacin kuds.
426369