IQNA

An Fara Gudanar Da Taro Kan Tsarin Banki Da Hannayen Jari A Musulunci

23:26 - July 10, 2009
Lambar Labari: 1799718
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro dangane da tsarin banki da saka hannayen jari a mahangar musulunci a kasar Austaralia, wanda cibiyar kula da harkokin tattalin arzikin musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na arab online cewa; An fara gudanar da wani zaman taro dangane da tsarin banki da saka hannayen jari a mahangar musulunci a kasar Austaralia, wanda cibiyar kula da harkokin tattalin arzikin musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar masana kan harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi da ma na wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba, inda suke yin bahasi dangane da matsalolin da da kasashen duniya ke fuskanta na harkokin tattalin arziki, tare da bayyana mahangar musulunci a kan dukkanin matsalolin tattalin arziki.

430964





captcha