IQNA

Za A Bude Wata Cibiyar Ilimin Fikihu A Cikin jami'ar Malazia

22:45 - July 17, 2009
Lambar Labari: 1802692
Bangaren kasa da kasa; Mataimakin shugaban jami'ar kere-kere da sana'oi ta kasar kasar Malazia da ke birnin Kualalmpor fadar mulkin kasar, ya bayyana cewa za a kafa wata cibiya ta musamman da za ta rika kula da ilimin fikihu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na jami'ar Malazia cewa; Mataimakin shugaban jami'ar kere-kere da sana'oi ta kasar kasar Malazia da ke birnin Kualalmpor fadar mulkin kasar, ya bayyana cewa za a kafa wata cibiya ta musamman da za ta rika kula da harkokin ilimin fikihu da musulmi ke bukatar sani a cikin jami'ar. Bayanin ya ci gaba da cewa, kafa wannan cibiya zai taimaka matuka wajen warware da dama daga cikin mas'aloli na fikihu da ake bukatar gudanar da nazari da bincike kansu, kasantuwar a cikin jami'oi babu irin wadannan cibiyoyi, hakan ya sa dalibai masu nazari kan ilimomin addinin musulunci musamman ma bangaren fikihu suna shan wahala wajen samun madogara a bahasin da suke gudanarwa.

434392
captcha