IQNA

An Saka Wa Wani Babban Titi Sunan Marwa sharbini A Kasar Masar

17:36 - July 18, 2009
Lambar Labari: 1803495
Bangaren kasa da kasa; An saka sunan Marwa Sharbini a kan wani titi da ke cikin birnin Iskandariya na kasar maser, domin tunawa da shahidiyar nan 'yar kasar Masar da ta yi shahada a kasar Jamus domin saka hijabin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP cewa; An saka sunan Marwa Sharbini a kan wani titi da ke cikin birnin Iskandariya na kasar maser, domin tunawa da shahidiyar nan 'yar kasar Masar da ta yi shahada a kasar Jamus domin saka hijabin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa gwamnan jahar Iskandariya Adil Labib ya bayyana cewa ya amince a saka sunan Marwa sharbini a kan wani babban titi da ke tsakiyar birnin domin tunawa da ita. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin makonnin da suka gabata ne aka kasha Marwa sharbini a kasar Jamus sakamakon rikon da ta yi da saka hijabin musulunci.

435173
captcha