Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Ofishin kungiyar harkokin kiwon lafiya a yankin gabas ta tsakiya ta sanar cewa ministocin harkokin wajen kasashen yankin za su gudanar da wani zama a birnin Alkahira na kasar Masar, dangane batun ayyukan haji da kuma yadda matakan da ya kamata a dauka domin kare lafiyar mahajjata. Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da zaman yana da matukar muhimmanci, domin kuwa tun bayan da cutar murar aladu ta bayyana aka shiga cikin halin dardar dangane da batun ayyukan haji da umra, domin kuwa wasu daga cikin malamai sun nuna cewa za a iya daga ayyukan haji da umra domin kaucewa kamuwar al'ummar musulmi daga wannan cuta. Wannan shi ne babban abin da zaman zai mayar da hankali kansa.
435594