Bangaren kasa da kasa; Minista mai kula da harkokin addinin musulunci a kasar Yeman ya bayyana cewa yanzu haka an fara aiwatar da wani shiri da gwamnatin kasar take da shi, na kafa cibiyoyin addinin musulunci kimanin 3000 a fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na mutamar net cewa; Minista mai kula da harkokin addinin musulunci a kasar Yeman ya bayyana cewa yanzu haka an fara aiwatar da wani shiri da gwamnatin kasar take da shi, na kafa cibiyoyin addinin musulunci kimanin 3000 a fadin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa ministan harkokin addini na kasar ya bayyana hakan ne a gaban wani taro na talafawa marayu da aka gudanar a birnin San'a na kasar Yeman, inda ya jaddada cewa wannan shirin na kafa wadannan cibiyoyi zai taimaka matuka wajen talafawa marayu da marassa karfi, kamar yadda shiri zai taimaka wajen ilmantar da marayu wajen sanin ilmomin addinin mulunci.
435472