IQNA

16:38 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1804352
Bangaren siyasa; Za a gudanar da taron mab'as na tunawa da zagayowar ranar da manzon Allah SAW ya yi mi'iraji daga hijaz zuwa birnin Qods mai alfarma, inda ya yi isra'i daga masallacin Qods zuwa sama, wanda za a gunar a hubbaren Imam Khomeini(RA) da ke birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren Imam Khomeini (RA) cewa; Za a gudanar da taron mab'as na tunawa da zagayowar ranar da manzon Allah SAW ya yi mi'iraji daga hijaz zuwa birnin Qods mai alfarma, inda ya yi isra'i daga masallacin Qods zuwa sama, wanda za a gunar a hubbaren Imam Khomeini(RA) da ke birnin Tehran.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar malamai masana kan ilmomin tarihi na cikin gida da wajen kasa, inda za a gabatar da jawabai da suka danganci mi'irajin manzon Allah da kuma darussan da suke tattare hakan, da kuma hikimar ubangiji madaukaki sarki.

436266Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: