IQNA

Babban Sakataren Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ya Jinjinawa Shugaban Kasar Rasha

16:35 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1804500
Bangaren kasa da kasa:Ikmalul Din Ihsan Uglan babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya jinjina wa Shugaban kasar Rasha Dimitare Madodef kan yadda ya ziyarci babban masallaci a birnin Masko.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta nakalto kungiyar hadin kan kasashen musulmi na watsa sakon babban sakataren kungiyar da a ciki yake jinjinawa shugaban kasar Rasha kan yadda ya nuna matsayinsa da daukakarsa da kai ziyara a babban masallaci a birnin Masko babban birnin kasar ta Rasha. Wannan yana nuni da yadda addinin musulunci ke kara samun gindin zama da matsayi a kasar ta Rasha a hukumce.

436509
captcha