IQNA

Daliban Makarantun Sakadanre Za Su Fara koyon Addini A Rasha

14:52 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805093
Bangaren kasa da kasa; Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya bayar da umurni ga ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasar Rasha cewa, a bayar da dama ga mabiya addinai da su koyi addininsu a makarantun sakandare na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran risalehaber cewa; Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya bayar da umurni ga ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasar Rasha cewa, a bayar da dama ga mabiya addinai da su koyi addininsu a makarantun sakandare na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar ta Rasha Dmitry Medvedev ya bayar da wannan umurnin ne domin bayar da dama kare hakkokin addinai a kasar, wanda hakan zai bayar da dama ga musulmi na kasar rasha su san addinin musulunci a hukumance, ta yadda za su fara sanin addini tun daga kuruciyarsu wato daga makarantun sakandare. Da dama daga cikin mabiya addinai na kasar sun nuna matukar gamsuwarsu da farin cikinsu da wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka.

437454

captcha