IQNA

13:45 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806348
Bangaren siyasa da zamantakewa; Za a gina wata babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a yankin Saida da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa da ke kasar labanan cewa; Za a gina wata babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a yankin Saida da ke kudancin kasar, da nufin yada harkokin tabligin musulunci da hada kan kungiyoyin musulmi da ke kasar domin yin aiki baki daya wajen yada addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar za ta mayar da hankali ne wajen yada addinin musulunci tare da bayyana hakikanin manufofinsa ga sauran al'ummomi musamman ma wadanda ba musulmi da ke yankin, bayan nan kuma za ta kafa wasu rassanta a wasu yankuna na kasar Labanan domin gudanar da ayyukanta.

438584

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: