Bangaren kasa da kasa; Tarukan da musulmi suke gudanarwa a masallacin Qods sun suna matukar girgiza yahudawan sahyuniya, a kan haka ya kamata musulmi su taru a cikin masallacin domin kalubalantar barazar rushe masallacin da yahudawa ke yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; Tarukan da musulmi suke gudanarwa a masallacin Qods sun suna matukar girgiza yahudawan sahyuniya, a kan haka ya kamata musulmi su taru a cikin masallacin domin kalubalantar barazar rushe masallacin da yahudawa ke yi. Bayanin ya ci gaba da cewa yahudawan sahyuniya suna barazanar rushe masallacin Qods wannan ne ya sanya shugaban kwamitin kula da harkokin masallacin qods din Ikrama sabri ya kirayi dukkanin palastinawa mazauna birnin Qods da su taru a masallacin a ranakun litinin da talata, domin hakan yana firgita yahudawa.
439516