IQNA

Za A Kammala Bangaren Farko Na Gasar Kur'ani Mai Tsarki A Masar

16:57 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825198
Bangaren kasa da kasa; A yau za a kammala bangare na farko na gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar kasar Masar al-yaum sabi cewa; A yau za a kammala bangare na farko na gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Alkahira na kasar Masar, wanda kuma wannan shi ne kar na bakwai da ake gudanar da irin gasar kur'ani a kasar masar. Bayanin ya ci gaba da cewa gasar karatun kur'anin tana samun halartar makaranta daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da kuma wasu makaranta da mahardata na cikin gida. Za a gudanar da gasar ne a cikin matakai guda uku, yanzu haka dai an kammala bangare na farko a cikin gasar. Minista mai kula da harkokin addini na kasar Masar ya ce gasar ta samu nasara kamar yadda ya kamata.

463456

captcha