Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na na kamfanin dillancin labaran reauters bangaren larabci cewa; Za a bude bankin musulunci a karon farko a kasar Kazakistan, wanda zai zama rehsen babban bankin musulunci na Alhilal da ke birnin Abu dabi na kasar hadaddiyar daular larabawa. Yanzu haka dai an zuba tsabar kudi a cikin bankin da za su dirhami miliyan dari na kasar hadaddiyar daular larabawa. Wasu daga cikin 'yan kasuwar kasar Kazakistan sun bayyana azamarsu ta tallafawa bankin da dukkanin karfinsu.465116