Daga kasar Labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ayatullah Abdul Amir Kablan a cikin wani sako ga Musulmi da larabawa ya bayyana cewa: duniyar larabawa da musulmi dole su zamanto tsintsiya madaurinki daya domin kubutar da Masallacin Kudus Mai Tsarki kuma kar su yi ogaro da kadaita da kawai mika sakon fatar baki ga gwamnatin danniya da wariya gami da wuce gonad a iri ba tausayi ta Haramtacciyar kasar Isra'ila.Na'ibin shugaban komitin koli na yan Shi'a a Labanon ya kara da cewa; musulmin da kiristoci domin kare abubuwa masu muhimmanci na musulmi da kiristoci a Palasdinu kamar masallacin Aksa ,cocin Alkiyma,masallacin Sukkhra da Masallacin Ibrahim Khalili sai su dauki matakin gwagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ila.
465857