Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kasar Pakistan cewa; Tawagar Iraniyawa makarantar kur'ani da suka isa kasar Pakistan domin raya ranakun karshe na watan Ramadan a kasar sun ziyarci karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Karachi. Tawagar Iraniyawan ta samu karbuwa a wajen al'ummar Pakistan, inda suka halarci tarukan addinin musulunci da ake gudanarwa a cikin wata Ramadan a biranan kasar Pakistan.467257