Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na jaridar alwatan ta kasar Saudiyya cewa; Musulmin kasar Amurka sun nuna rashin amincewa da wasu jawabai da aka gabatar da ke nuna goyon baya ga zanen batunci ga manzon Allah, wanda wani dan kasar danmar ya yi. Bayanin ya ci gaba da cewa Musulmin kasar Amurka daga kowane bangare na kasar sun yi kakkausar suka dangane da hakan, inda suka bayyana hakan da cewa wani hankoro ne na haddasa kyamar addinin musulunci da musulmi a kasashen yammacin turai. 470437