IQNA

Yahudawa Sun Hana Wadanda Ba Musulmi Ba Shiga Masallacin Annabi Ibrahim (AS)

17:00 - October 05, 2009
Lambar Labari: 1833915
Bangaren manema labarai: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana wadanda ba yahudawa ba shiga masallacin Ibrahim (AS).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Ina ta watsa rahoton cewa; Zaid Alja'abiri shugaban da ke kula da harkokin addini ya bayyana cewa" sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana musulmi da wadanda ba yahudawa ba shiga cikin masallacin Annabi Ibrahima (AS) da hakan ke nuni da yadda mahukumtan Haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da take hakkin bil adama da kuma hakkin yin addini da dokokin kasa da kasa suka ba wa kowa dama cikin sauki da walwala amma ba haka lamarin yake bag a Palasdinwa da aka mamaye masu yanki.

473947


captcha