IQNA

An Kera Wata Na'urar Digitarl Mai Karatun Kur'ani A Amurka

12:59 - October 21, 2009
Lambar Labari: 1840081
Bangaren kasa da kasa; An kera wata na'urar digital da ke dauke da karatun kur'ani mai tsarki wadda ake yin amfani da ita a cikin motoci.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na na na'urorin da ake kerawa domin yin amfani da su a cikin motoci masu dauke da sauti na Amurka cewa; An kera wata na'urar digital da ke dauke da karatun kur'ani mai tsarki wadda ake yin amfani da ita a cikin motoci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na'ura tana dauke da sauti da kuma wasu fayafai masu dauke da hotuna, duk dai dangane da karatun kur'ani mai tsarki. Ana sa ran za a yada wannan na'ura a cikin kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi. 481363
captcha