Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; An umurci ma'aikatan gwamnatin kaar Indonesia da su koyi karatun kur'ani mai tsarki a lardin Grinlano na kasar. Bayanin ya ci gab ada cewa mahukuntan lardin sun bayar da wannan umurni ne da nufin kara karfafa ma'aikatan gwamnati wadanda akasarinsu musulmi ne su koyi karatun kura'ni, domin hakan ne zai ba su damar sanin abin day a kamata su aiikata da bai sama ba ka'ida ta musulnci. 481312