Bangaren kasa da kasa; Ana kawata gine-ginen makarantu da jami'oin Chechniya da rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki, da nufin saka tunanin kur'ani da addinin muslunci a cikin zukatan kanan yara da matasan yankin.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da Firaministan Chechniya Ramezan Kadiruv ya bayyana cewa; Ana kawata gine-ginen makarantu da jami'oin Chechniya da rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki, da nufin saka tunanin kur'ani da addinin muslunci a cikin zukatan kanan yara da matasan yankin. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da cewa al'ummar Chechniya musulmi ne masu son addinin Musulunci, wannan ya sanya gwamnatinsa daukar matakai na raya addini tare da farfado da martabarsa a yankin, musamman ma ga kanan yara da matasa.481281