Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Qatar cewa; An fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya a birnin Doha na kasar Qatar, da nufin kara kusanto da fahimta tsakanin dukkanin mabiya addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai mayar da hankali kan irin muhimmancin da ke tattare da yin aiki tare tsakanin addinai domin tabbatar da fahimtar juna da samun zaman lafiya a duniya. 481936