Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na tashar talabijin ta Rasid cewa; Gwamnatin Saudiyya mai bin akidar wahabiyanci ta hana mabiya mazhabar shi'a gina masallaci da kuma makabarta da za su rika yin amfani da ita wajen rufe wadanda suka rasa daga cikinsu daidai da koyarwar mazhabar iyalan gidan manzon Allah. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba shi ne karon farko da mahukuntan kasar Saudiyya suke daukar irin wannan mataki na ta'assubanci a kan mabiya mazhabar shi'a ba, amma kuma duk da haka gwamnatin kasar bat a taba fuskantar wani matsin lamaba daga kasashen yammacin turai kan wannan mummuna aiki ba. 482051