Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; Wata makaranciyar kur'ani bairaniya da ta halarci gasar hardardar kur'ani da hadisan ma'aiki da aka gudanar a birnin Sharja na hadaddiyar daular larabawa ta samu zuwa matsayi na biyu a gasar. Bayanin ya ci gaba da cewa an bayar da kyaututtuka ga wadanda suka samu matsayi na daya da na biyu da na uku a kowane bangare na gasar. 482667