IQNA

Za A Gudanar Da Wani Baje Koli Kan Aikin Hajji A Madina

19:47 - October 25, 2009
Lambar Labari: 1841522
Bangaren kasa da kasa; Magajin garin birnin Madina Abdulaziz Bin majid ya bayyana cewa, za a gudanar da wani baje koli kan ayyukan hajji a masallacin manzon Allah da ke birnin Madina har na tsawon mako guda.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Nasij a shafinsa na internet cewa; Magajin garin birnin Madina Abdulaziz Bin majid ya bayyana cewa, za a gudanar da wani baje koli kan ayyukan hajji a masallacin manzon Allah da ke birnin Madina har na tsawon mako guda.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje zai taimaka wajen bayyana wa maniyyata muhimman abubuwa da suka danganci aikin da kuma tarihinsu gami da asalinsu. 482899


captcha