Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da zaman taro kan hakkoki a mahangar addinin muslunci, wanda cibiyar kula a harkokin nazari da bincike kan addinin musulunci ta kasar Birtaniya ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dilalncin labaran socio cewa; Za a gudanar da zaman taro kan hakkoki a mahangar addinin muslunci, wanda cibiyar kula a harkokin nazari da bincike kan addinin musulunci ta kasar Birtaniya ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo da cibiyar take shirya gudanar da irin wannan zaman taro, kuma taron zai samu halaryat masana daga sassa daban-daban na kasashen turai da na muslmi musamman ma masana daga cikinsu. 482873