Kamfanin dillancin labarann Iqna ya nakalto daga shafin internet na Islamic events cewa; Jamia'r birnin Bruccel na kasar Belgium za ta dauki nauyin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan rayuwar mabiya addinin Musulunci a nahiyar turai, da kuma 'yancin addini da ake rayawa a nahiyar da kuma yadda musulmi suke samun wannan 'yanci. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai bahasi kan yadda ake takura wa musulmi a nahiyar turai. 483077