Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na nice cewa; Za a Gudanar Da Wani zaman taro kan hakkokin musulmin kasar faransa, da yadda suke samun damar gudanar da harkokin addininsu a kasar. Jamia'r birnin Paris na kasar za ta dauki nauyin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan rayuwar mabiya addinin Musulunci a nahiyar turai, da kuma 'yancin addini da ake rayawa a nahiyar da kuma yadda musulmi suke samun wannan 'yanci. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai bahasi kan yadda ake takura wa musulmi a nahiyar turai. 482978