IQNA

Jami'oin Kasashen Turai Za Su Gudanar Da Taruka Kan Hakkokin Musulmi

19:48 - October 25, 2009
Lambar Labari: 1841536
Bangaren kasa da kasa; Musulmi a nahiyar turai su ne marassa rinjaye da suka fi fuskantar matsaloli daga mazauna kasasashen nahiyar na asali wadanda ba mabiya addinin Musulunci neb a.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Sociorel cewa; Musulmi a nahiyar turai su ne marassa rinjaye da suka fi fuskantar matsaloli daga mazauna kasasashen nahiyar na asali wadanda ba mabiya addinin Musulunci ne ba. Jamia'r birnin Paris na kasar za ta dauki nauyin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan rayuwar mabiya addinin Musulunci a nahiyar turai, da kuma 'yancin addini da ake rayawa a nahiyar da kuma yadda musulmi suke samun wannan 'yanci. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai bahasi kan yadda ake takura wa musulmi a nahiyar turai. 482976


captcha