IQNA

Yan jami'ar Hatak Sun Yi Allah Wadai Da Matakin Muzanta Kur'ani

13:33 - October 28, 2009
Lambar Labari: 1842322
Bangaren siyasa da zamantakewa;daruruwan yan jami'a ne a birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da yadda sojojin Amerika ke cin zarafin kur'ani a wannan kasa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta watsa rahoton cewa:daruruwan yan jami'a ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai a birnin Kabul domin kalubalanta da nuna rashin jin dadinsu kan yadda sojojin Amerika a wannan kasa ke cin zarafin kur'ani mai girma da kuma yadda suke muzgunawa musulmin wannan kasa.Masu gudanar da wannan zanga-zanga dai sun yi tar era taken Allah tsine da tofin Allah tsine a fili karara.

483680
captcha