IQNA

Al'ummar Brazil Na Matukar Bukatar Samun Masaniya Kan Musulunci

13:28 - October 28, 2009
Lambar Labari: 1842337
Bangaren kasa da kasa; Babban editan jaridar kasar Brazil ta Folha ya bayyana cewa; al'ummar Brazil suna da matukar sha'awar sanin addinin Musulunci da koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa Babban editan jaridar kasar Brazil ta Folha ya bayyana cewa; al'ummar Brazil suna da matukar sha'awar sanin addinin Musulunci da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa editan jaridar ta Folha ya bayyana hakan ne a tarukan baje kolin kayan sadarwa da ake gudanarwa a nan birnin Tehran, wanda ke samun halartar kafofin yada labarai daga sassa daban-daban na duniya. 483452
captcha