Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Umma united cewa; Za a gudanar da wani zaman taro da nufin shiga yaki da akidar nan ta kyamar addinin Musulunci a kasashen yammacin turai, wanda za a gudanar a birnin Toolz na kasar faransa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Faransa da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi da suke kiyayya da wannan akida. 483853