Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na alkuthar cewa; Za a gudanar da wani zaman taro domin yin bahasi kan lamurra da suka danganci aure a mahangar addinin Musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin musulmi da zamantakewarsu a kasar Birtaniya ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan zaman taro a babban dakin shirya taruika na jami'ar Wales da ke Birtaniya. 484134