Bangaren kasa da kasa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta yi Allawadai da hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Bagdaza, da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren kula da harkokin jam'a da kafofin yada labarai na kungiyar ISESCO cewa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta yi Allawadai da hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Bagdaza, da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba komai ba ne illa neman mayar cda hannu agogo baya a lamurran siyasa akasar Iraki. 484141