Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wata zantawa da bangaren yada labaransa ya gudanar tare da ministan mai kula da harkokin sadarwa na kasar Iran ya bayyana cewa; Kafofin yada labarai suna da gagarumar rawar da za su iya takawa ta fuskoki da dama domin ciyar da tunanin al'mma a gaba kan koyarwar kur'ani. Ya ci gaba da cewa yana da matukar muhimmanci ga masu kula da yada labarai a kasashen musulmi. 483996