Bangaren kasa da kasa; A karon farko za a gudanar da wani zaman taro kan kayyaki na halal a mahangar musulunci a nahiyar turai, wanda cibiyar kula da kayyaki halal ta shirya gudanarwa a birnin Hague na kasar Holland.
Kamfanin dillancin labarin Iqn aya nakalto daga kamfanin dillancin labaran world halaforum cewa; A karon farko za a gudanar da wani zaman taro kan kayyaki na halal a mahangar musulunci a nahiyar turai, wanda cibiyar kula da kayyaki halal ta shirya gudanarwa a birnin Hague na kasar Holland. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman batutuwa da suka fi daukar hankali a cikin shirye-shirye da cibiyar take gudanarwa. 485399