Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Tawagar farko ta alhazai daga yankin Zirin Gaza a Palatinu ta isa kasa mai tsarki a jiya bayan da suka bi ta hanyar Rafah dake iyaka da yankin da kuma kasar Masar.Bayanin ya ci gaba da cewa wanda ke jagorantar tawagar alhazan Talib Abu sha'ari ya bayyana cewa adadin wadanda suka tafi hajin daga Gaza ya kai mutane 1000, kuma ana sa ran adadin wadanda za su je hajjin bana daga Gaza zai kai mutane 4500, inda sauran za su rike su a hankali. 488664