Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa da ke tare da lahazai a kasa mai tsarki cewa; Kimanin alhazai Iraniyawa 23000 ne za su halarci taron addu'ar Komail a haramin manzon Allah (SAW) a Madina a mako na biyu a jere.
Bayanin ya ci gaba da cewa masu ziyara suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na ziyara a birnin Madina mai alfarma, inda suke ziyartar manzon Allah da iyalan gidansa da kuma salihai daga cikin sahabbansa. 491476