Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a cikin wata zantawa da ta hada shi da wani babban malamin jami'a da ke birnin Kualalampour na kasar Malazia Shamsuddin Aref, ya bayyana cewa; Masana daga cikin musulmi na wannan zamani dole ne su safke nauyin da ya rataya kansu na kara wayar da kan mutane dangane da hakikanin koyarwa irin ta addinin Musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman abubuwan day a kamata a mayar da hankali kansu wajen tantance batutuwa da suka dangaci koyarwa irin ta addinin Musulunci. 492149