Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi cewa; babban sakataren kungiyar ya tabbatar da cewa barranta daga mushrikai babban bangare ne na aikin hajji da baya gushewa a kowane lokaci duk kuwa da canjin yanayin duniya da muke rayuwa a cikinta a halin yanzu. Ya kara da cewa babu wani wanda zai iya raba rukunin haji na barranta daga mushrikai da sauran rukunan hajji. 493944